NDLEA ta kama mutane 198 da ake zargi da safarar kwayoyi a Kano.

 NDLEA ta kama mutane 198 da ake zargi da safarar kwayoyi a Kano


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tare da tarwatsa mahadar da ake tattaruwa don safarar miyagun kwayoyi guda 21 a Kano.


Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar a jihar Kano Sadiq Muhammad-Maigatari ya raba wa manema labarai a Kano.


Ya ce an kama su ne a tsakanin 17 zuwa 26 ga watan Janairu, a cikin shirin hukumar na “Operation Hana Maye” da Kwamandan Hukumar Abubakar Idris-Ahmad ya kaddamar domin yaki da shaye shaye.


A cewarsa, daga cikin mutane 198 da aka kama, 177 maza ne, 21 kuma mata ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp