Gwamnatin Nasarawa ta musanta sanya hannu wajen kafa kungiyar ’yan banga ta Fulani a jihar.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta da hannu wajen kafa kungiyar ’yan banga ta Fulani da aka kafa kwanan nan a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin kakakin majalisar, Danladi Jatau domin taya shi murna bisa samun nassara da yayi a kotun koli a fadar gwamnatin jihar.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta zaman lafiya a jihar,inda jaddada cewa tuni jami’an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin ‘yan banga na Fulani.
Ya ce da a ce matakin daga gwamnati ne, da an aika da kudirin dokar ga majalisar dokokin jihar domin tantance wa saboda haka basuda wata masaninya akan kaddamar da yan bangar.