'Yan ta'adda sun bude wuta kan motoci sama da 20 a Katsina, sun kashe mutane akalla 6


'Yan ta'adda sun bude wuta kan motoci sama da 20 a Katsina, sun kashe mutane akalla 6

'Yan ta'adda sun bude wuta kan motocin da suka fito daga garin Mai Dabino zuwa 'Yantumaki a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma'ar nan, a daidai lokacin da mutanen suka baro garin Mai Dabino kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a Yantumaki.

Majiyar ta sanar cewa dama duk mako sai sun yi ayari sannan jami'an tsaro su raka su zuwa cin kasuwa a garin 'Yantumaki da kasuwar ke ci duk Juma'a.

Wani direban mota da DCL Hausa ta zanta da shi ya shaida cewa an kona wasu daga cikin motocin da suke tafe da su. Sannan mafiyawan wadanda suka tagayyara ta dalilin bude wutar su ne mata da kananan yara.

Direban ya sanar cewa akwai ma wani babban soja daga cikin wadanda suka rako su da ya samu harbin bindiga har an garzaya da shi asibiti.

1 Comments

Previous Post Next Post