Hukumar Hisba a jihar Katsina ta ja kunnen iyaye akan su kula da yaransu, kuma su ja kunnensu kafin su fara kai samame a gidajen baɗala a jihar.
Kwamandan hukumar Sheikh Aminu Usman Abu-Ammar ne ya faɗi hakan a cikin wani faifan bidiyo yana mai cewa duk mahaifin da ya san ɗansa yana tattara daba a cikin unguwanni, to su kuka da kansu.
Abu-ammar ya ce duk ɗan da ya kuskura ko mahaifin da ya sake ya shigo hannun hukumar zai fuskanci fushin hukuma.
"Zamu shiga lungu da sako domin mu tsawatar, ayi dai-dai"
"Aikin hukumar Hisba ne umarnin da kyakkyawa da kuma hani da mummuna, wannan shi ne jigon aikin hukumar'
Ya kara da cewa "Manufar hukumar shi ne a taimake ka ɗan ka ya zama ingantacce, saboda nauyi ne na hukuma ta yi aikin da za ta inganta al'ummar da take jagoranta."
Kwamandan ya kara da cewa hukumar za ta yi kokari wajen taƙaita barace-batace a bisa titunan jihar.