EFCC ta kai samame a ofishin DangoteJami'an hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC sun kai wani samame a babban ofishin kamfanin Dangote a jihar Legas.

Jaridar Premium Times ta ruwaito, jami'an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun gudanar da bincike kan canjin kudin da aka ware wa kamfanin a zamanin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele.

Jami'an na EFCC sun bukaci takardun da ke dauke da bayanan kudaden ketare da bankin CBN ya ba kamfanin a cikin shekaru goma da suka gabata.

Idan dai baku manta ba a watan Disamba na shekarar da ta gabata wani mai binciken kwakwaf ya bankado wasu asusun banki guda 593 da ke a kasashen waje.

Post a Comment

Previous Post Next Post