Ministan tsaro Matawalle ya gabatar da jiragen ruwa marasa matuki ga Tinubu

 


Ministan kasa a Ma'ikatar Tsaron Nijeriya Mohammed Bello Matawalle, ya gabatar ma Shugaban kasa Bola Tinubu jiragen ruwa marasa matuki guda biyu a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai Henshaw Ogubike ya fitar a Abuja.

Sanarwar ta ce Ministan ya shaida wa shugaban kasa cewa, Jiragen biyu za su taimaka wajen yaki da ta’addanci a bakin gabar ruwa.

Matawalle ya sanar da Tinubu cewa wadannan jirage na da nufin inganta sabbin fasahohin da za su kara wa sojojin Najeriya kwarin gwiwa wajen tunkarar kalubalen tsaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post