Matakin gwamnati kan digiri 'dan Kwatano' ya shafi daliban Nijeriya 15,000


Ƙungiyar ɗaliban Najeriya (NANS) a jamhuriyar Benin ta bayyana cewa sama da dalibai 15,000 ne suka shiga halin kaka-ni-kayi, sakamakon haramta wasu jami'o'i da gwamnatin Nijeriya ta yi a kasar.

Shugaban ƙungiyar a Jamhuriyar Benin, Ugochukwu Favor, ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels.

A yayin tattaunawa Favor ya yi kira da a sassauta wannan mataki musamman a kasashe Benin da Togo.

Hakan dai na zuwa ne bayan da wani ɗan jarida mai binciken kwakwaf ya fallasa yadda ake samun takardar shaidar kammala makarantun a kasashen.

Shugaban kungiyar daliban ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi bincike mai zurfi don gano wadanda ke da hannu a badakalar kuma a hukunta su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp