Jirgin yakin soji a Nijar ya yi hatsari

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar ne janar Salifou Mody ya sanar da faduwar jirgin mai saukar angulu na dakarun kasar a yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga wani aikin sintirin hadin gwiwa da askarawan Burkina Faso

Sanarwar ministan ta ce da misalin karfe 12 na ranar Juma'ar nan ce 5 ga watan Janairu ne hatsarin jirgin ya auku sakamakon matsalar na'ura a daidai lokacin da yake shirin sauka a filin jirgin sojoji na Kantchari

Babu wanda ya rasa rai dai a wannan hatsari amma sai karamin rauni da mutum daya ya samu kamar yadda sanarwar ta ambato

Post a Comment

Previous Post Next Post