Ba zamu amince da kasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba-NLC


Kungiyar kwadago ta Najeriya ta mayarwa da shugaban kasar martani kan alkawarin sa na sabuwar shekara game da shirin yiwa ma’aikatan kasar karin albashi.

Kungiyar karkashin jagorancin Joe Ajero ta ce babu wani dalili da zai sa ta amince gwamnatin tarayya ta yi gaban kanta wajen Karin albashi, a wannan karo ya zama wajibi a tattauna da su kafin karin albashin.

Shekarar 2018 ce shekara ta karshe da gwamnatin tarayya ta tattauna da kungiyar kwadago kafin kara albashi.

Kungiyar ta ce gwamnati ta jima tana yi mata dadin baki game da karin albashi, sai dai a wannan karon ya zama wajibi ta dauki mataki, don shiga yarjejeniya da gwamnatin tarayya a watan Afrilu mai zuwa.

Sai dai babban abinda ya fi daukar hankali a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar shine, yadda ta ce ba zata amince da kasa da naira dubu 200 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Al’ummar Najeriya sun fada cikin halin masti tun bayan da gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur da yadda darajar naira ke kara sulalewa, yayin da kayan masarufi ke kara tsada dalili kenan da ya sa kungiyar kwadagon ke ganin bai kamata ma’aikata su rika karbar kasa da naira dubu 200 a matsayin albashi ba.

 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post