Ministan ayyuka a Nijeriya Sen. David Umahi, ya ce kamfanin Julius Berger na neman karin Naira Tiriliyan N1.35tr domin kammala aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano.
Ministan ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manyan Daraktocin ma'aikatar ayyukan jawabi a ranar Alhamis.
Aikin dai na daya daga cikin ayyukan da gwamnatin Shugaba Tinubu ta gada daga tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari.
Category
Labarai