An kai kudirin neman majalisa ta amince 'yan Nijeriya su rika kare kansu daga ta'addanci

Majalisa

Majalisar dattawan Nijeriya za ta tattauna kan kudirin da zai ba 'yan kasa damar mallakar makamai domin kare kansu.

Jaridar Leadership ta ruwaito sanata mai wakiltar Delta ta Arewa a majalisar Prince Ned Nwoko ne ya gabatar da kudirin dokar, domin yin gyara a dokar da ake da ita ta mallakar makami ga farar hula.

Ya kara da cewa barazanar tsaro da 'yan kasa ke fuskanta ya sa mutane da yawa cikin halin kunci da rashin kwanciyar hankali inda ya kara da cewa kudirin nasa zai baiwa fararen hula damar mallakar makamai da za su kare kansu.

Daga karshe Sanatan ya yi fatar abokan aikin nasa za su goyi bayan kudirin.

Post a Comment

Previous Post Next Post