Sadiya Umar Faruq ta fadi dalilin da ya sa ba ta je ofishin EFCC ba

Tsohuwar ministar jin kai a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, Sadiya Umar Faruq ta ce rashin lafiya ne babban dalilin da ya hana ta girmama gayyatar hukumar EFCC.

Punch ta rawaito cewa, Sadiya Umar Faruq ta rubuta wa EFCC a hukumance neman alfarmar a kara mata wa'adi kan gayyatar da hukumar ke yi mata.

Ana dai tuhumar Sadiya Umar Faruq kan wasu kudi da suka kai Naira bilyan 37 da ake zargin sun yi batan-dabo a ma'aikatar a lokacin da take matsayin minista hadin baki da wani dan kwangila mai suna James Okwete.

Jaridu dai sun buga labarin cewa jami'an EFCC na can na neman takardar iznin kamo tsohuwar ministar Sadiya Umar Faruq tun da ta ki mutunta gayyatarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post