An samu Gwamna a Nijeriya da ya kiyasta kashe N702m kan abinci da nishadi


Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya saka Naira milyan 702 a matsayin da za a kashe wajen sayen abinci da kuma samar da nishadi a ofishinsa da na Sakataren Gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ware wadannan kudaden ne a cikin daftarin kasafin kudin shekarar 2024 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Kwamishinan tsare-tsaren kasafin kudi Ademola Adeleke wanda ya tabbatar da labari a lokacin kare kasafin kudi, ya musanta cewa an ware Naira bilyan 11 don biyan wadannan bukatun.

Kwamishinan ya ce an ware Naira bilyan 8 don gudanar da ayyukan yau da kullum a ofishin Gwamna da sassan da ke karkashin ofishin.

Post a Comment

Previous Post Next Post