EFCC na neman iznin kamo tsohuwar ministar jin kai a gwamnatin Buhari, Sadiya Umar Faruq

Jami'an hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa tu'ammati EFCC na duba yiwuwar neman takardar iznin kamo tsohuwar ministar jin kai a gwamnatin Buhari, Sadiya Umar Faruq.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa hakan ya biyo bayan kin amsa goron gayyatar da hukumar ta yi mata a ranar Laraba.

Sadiya Umar Faruq dai da hukumar ta shirya karbar bakuncinta da misalin karfe 10 na safiyar Laraba, ana tuhumarta da batun wasu kudi da suka kai darajar sama da Naira bilyan 37.

Ana dai zargin cewa an wawure wadannan kudaden a zamanin da take minista ta hannun wani dan kwangila Mr James Okwete.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp