'Ya'ya da jikoki ne kadai za su iya biyan bashin da ake bin kasashen Afrika - Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce irin tarin bashin da ake bin kasashen Nahiyar Afrika, 'ya'ya da jikoki ne ya kamata su mayar da hankali wajen biyan wannan bashin.

Tsohon shugaban kasar ya ce, idan aka yi la'akari da wannan bashin, babu abin da ya dace a yi a nan gaba, illa a biya don ceto Nahiyar daga halin da ba a fatar ta shiga.

Obasanjo ya ce bashin da gwamnatinsa ta ciyo na Paris Club, gwamnatin da ta gaje shi ba ta ririta shi yadda ya kamata ba. Ya kara da cewa hakan ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.

Ya ce bashi wani dodoridi ne da ake yi wa kasashen Afrika, amma dai ya ce shugabanci ne babbar matsalar kasashen Nahiyar Afrika.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp