'Yan siyasa ne ke dagula harkokin zabe a Nijeriya - Ganduje



Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya yi kukan cewa da yawa daga cikin 'yan siyasar kasar ne ke dagula lamurran zabukan da ake gudanarwa.


Ganduje na magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin daraktar sa ido kan harkokin zabe da jam'iyyun siyasa Hawa Habibu, inda ya ce yana sane cewa babbar matsalar gudanar da zabe a Nijeriya ita ce batun tsaro, amma ba haka bane, 'yan siyasa ne babbar matsalar.


Ya ce akwai bukatar hukumar zabe INEC ta bullo da tsarin fadakar da jama'a kan illolin yin karan-tsaye ga harkokin zabe.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp