Buhari ya gaza samar da tsaro a tsawon shekaru, Tinubu na neman nanata irin kuskuren - Peter Obi


Dan takarar shugabancin Nijeriya a jam'iyyar LP a zaben 2023 Mr Peter Obi ya ce tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ya gaza samar da tsaro a kasar nan cikin shekaru 8 da ya shafe yana mulkar kasar.

Peter Obi ya kara da cewa abin takaici, yanzu kuma shugaba Tinubu ba neman nanata irin wannan kuskure na gaza samar da tsaro bayan da karbi jagorancin kasar.

Ya yi kira ga gwamnatin da ta nutsu ta bullo da hanyoyin samar da tsaro a lungu da sako na kasar nan.

Peter Obi dai na magana ne kan sabbin hare-haren da ke neman kunno kai musamman a sassan birnin tarayya Abuja.


Post a Comment

Previous Post Next Post