Kwastam sun kama taba sigari, giya, ashana da shaken 'amuru'



Jami'an tsaron hadin guiwa da ke sintirin kan iyakokin kasar nan da ke kula da arewa maso yamma sun sanar da cewa sun yi nasarar kama katan 34 na taba sigari da kwalaben giya.

Kazalika, jami'an sun kuma kama tirela shakare da ashana ta kasar waje da kuma tirela makare da dilolin shadda.

Kwantrolan kwastam da ke kula da shirin Mr IK Oladeji ya sanar a Katsina cewa jami'an sun kuma you nasarar katan 56 na sonadarin mimido da katan 76 na kuskus da ma tirela cike da dilolin gwanjo.

Ya kara da cewa a cikin jihohi 7 da shirin ke kula da shi, an yi nasarar kama 'yan kasashen waje 21 da suka yi yunkurin shigowa Nijeriya ba bisa ka'ida ba, ta kasar Nijar duk kuwa da sanar da rufe boda da aka yi bayan juyin mulkin soji.

Kwastam din sun sanar cewa sun kuma kama katan 32 na maganin mura wato syrup da buhunan tabar 'amuru' da ake shake da ita da ma katan 39 na taliyar spaghetti.

Kazalika, kamen na kwastam bai tsaya nan ba, sai da suka sanar da cewa sun kama katan 1,700na maganin feshin gona da jarkokin man girki 10 da dilolin gwanjo da kuma katan 82 na alawar tsotsa ta lollipop.

Kwantrolan kwastam IK Oladeji ya kara da cewa jami'ansa sun kuma kama buhunan shinkafa 132, sannan sun yi gwanjon man fetur jarkoki 60 da suka kama ga al'ummar jihar Katsina da aka sayar musu kan farashi mai rahusa da ya ce tuni sun saka kudin a asusun gwamnatin tarayya.

Ya ce kudin dutin kayan da aka yi nasarar kamawa cikin makonni biyu daga 2 zuwa 17 ga Janairu, sun kai Naira bilyan 1.2bn

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp