Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na farko a 2024

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jagoranci taron farko na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) bayan hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

Taron wanda ake gudanarwa a fadar shugaban kasa ya samu halartar ministoci da sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da kuma shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya.

NAN ta ruwaito cewa kafin a fara taron FEC, shugaban ya rantsar da Desmond Akawor a matsayin kwamishinan tarayya mai kula da tattara kudaden shiga, rarrabawa da kuma kasafin kudi (RMAFC).

An nada sabon kwamishinan tarayya na RMAFC, bayan rasuwar tsohon kwamishinan RMAFC na tarayya daga Rivers, Asondu Temple, a ranar 1 ga Nuwamba 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post