Za a kashe N32bn don kwaskwarima ga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro


Kimanin watanni 8 kenan da gina katafaren ginin da a yanzu haka hukumar kula da harkokin tsaro ta kasa ta ware Naira biliyan 31.915 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin yin sabbin gine-gine.

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun yawaitar kashe-kashe da sace-sacen al'umma a wasu jihohin Nijeriya, ciki har da babban birnin tarayya Abuja, inda 'yan bindiga ke sace jama’a daga gidajen su da wuraren kasuwancinsu.

A ranar 21 ga Maris, 2023, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da katafaren ginin ofishin harkokin tsaron na kasa da Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC), wadanda suka lakume biliyoyin Nairori.

A lokacin da yake kaddamar da wasu cibiyoyi guda biyu na zamani a Abuja, ya ce an yi su ne don inganta da magance matsalolin tsaro a kasar nan, musamman ta’addanci ayyukan bata gari.

Sabbin gine-ginen suna dauke da manya-manyan ofisoshi tareda babban dakin taro da cibiyoyin nazari da bincike.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp