Wani fasinja ya gartsawa ma'aikaciyar Jirgi cizo.

 Fasinja ya gartsa wa ma'aikaciyar jirgin sama cizo


Wani jirgin sama a kasar  Japan da ke kan hanyarsa ta  zuwa Amurka ya koma birnin Tokyo bayan da wani fasinja da ya bugu da giya ya ciji wata mata ma'aikaciyar jirgin da hakan ya tilasta wa matukin jirgin saukar gaggawa.


An ruwaito cewa mutumin mai shekaru 55 da ake kyautata zaton Ba’amurke ne, ya ciji matar a  hannunta, inda har ya ji mata  rauni, kamar yadda mai magana da yawun kamfanin All Nippon Airways ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP.


Lamarin da ya sa matukan jirgin da fasinjoji 159 suka  zuwa filin jirgin Haneda, inda aka mika mutumin ga ‘yan sanda. 


Kafar yada labarai ta kasar Japan TBS ta ruwaito fasinjan yana fadawa masu binciken cewa "bai san ya aikata laifin ba".

Post a Comment

Previous Post Next Post