Gwamnatin Kano zata kashe Biliyan 8 wajen gina makarantun firamare 3.

 Gwamnatin jihar Kano za ta kashe N8bn a makarantun firamare guda 3.




Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8 domin gina manyan makarantun firamare guda uku a fadin jihar.


 A cewar Gwamna Abba kabir Yusuf, makarantun za su kasance da cikakkun wuraren karatu, wanda hakan zai ba da isasshen yanayi ga yaran da suka fito daga sassa daban daban da zasuyi karatu a makarantun don samun ingantaccen ilimi da samun ci gaba. 


Gwamnan ya ce za a samar da manyan makarantun ne a Yankuna Uku dake jihar kuma za'a samar da kayayyakin koyo na zamani don samar da ingantaccen Ilimi a makarantun. 


Ya kuma ce an ware naira biliyan 6 domin gyara dukkan makarantun firamare dake jihar. 


 Yace gwamnati ta amince da gyara wasu cibiyoyi na musamman guda 26 da tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya kirkiro dasu a lokacin gwamnatin sa kuma an kammala 17.



"Za mu ci gaba da ba da kulawa ga samar da kayan aikin koyarwa na yau da kullum dazai ba wa yaranmu damar samun ingantaccen yanayin koyo da koyarwa a jihar kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp