'Yan sandan Katsina sun kuɓutar da mutane 171 daga hannun 'yan bindiga a 2023

CP Aliyu Abubakar Musa

Rundunar yan sanda jihar Katsina tace ta kuɓutar da mutane 171 waɗan da yan bindiga suka yi garkuwa dasu a jihar.

Mai magana da yawun rundunar Yan sandan jihar Katsina, SP Sadiq Abubakar ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar.

Abubakar yace rundunar ta samu nasarori a shekarar dubu biyu da ashirin da uku data gabata, ta kama mutane 1627, ta miƙa mutane 855 a gaban kuliya.

Haka zalika rundunar tayi nasarar kama mutane 258 bisa zargin su da aikata laifukan sata a jihar.

1 Comments

Previous Post Next Post