Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Halima Shehu, ko’odinetar shirin da ke kula da harkokin zuba jari ta kasa, sakamakon almubazzaranci da kudade.
Wannan na zuwa ne bayan watanni biyu da Majalisar Dattawa ta tabbatar da ita a matsayin kodinetan NSIPA na kasa.
Idan za'a tuna cewa a ranar 12 ga Oktoba 2023, shugaba Tinubu ya amince da nadin Halina Shehu.
Bayan dakatarwar da bincike kan zargin, an nada Dr Akindele Egbuwalo, Manajan Shirye-shiryen N-POWER na kasa a matsayin NC/CEO, har sai an kammala binciken.
Category
Labarai