Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 100 domin ciyar da makarantu, a cikin kasafin kudin shekarar 2024.
Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake rattaba hannu a kan kasafin kudi na shekarar 2024 da ya zama doka a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ya ce tanadin zai kara karfafa yan makaranta su cigaba da halartar makarantun su da kuma rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.
“Daya daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin kudirin dokar da aka amince da su kwanan nan shi ne ware Naira biliyan 100 don ciyar da yara ‘yan makaranta. Na yi imanin wannan zai zama abin ƙarfafawa ga shiga makarantu da kuma taimakawa wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ɗalibai.
Category
Labarai