Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane uku da ake zargin barayin mota ne tare da kwato wasu motoci da aka sace a Zariya.
Bayanin hakna na kunshe a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya raba wa manema labarai.
Sanarwa ta ce jami’an rundunar ‘yan sandan birnin Zariya ne suka yi wannan nasara bayan da suka yi aiki da sahihan bayanai suka kama barayin da ake zargi a Agoro da ke Tudun Wada Zaria.