'Yan Nijeriya na bukatar cikakken bayani kan bashin Dala bilyan 3.3 na kamfanin NNPC.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya kan bashin gaggawa na dala biliyan 3.3 na biyan danyen man fetur, Inda yabayyana cewa yan Nijeriya na bin gwamnati bayani akan batun bashin.

Atiku ya bayyana hakanne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a abuja inda yake cewa kamata yayi gwamnati ta dunga fito da bayanai da al'ummar kasa zasu fahimta bawai tayi shiru ba. 

Gwamnatin tarayya dai tun a shekarar da ta gabata, 16 ga watan Agusta, 2023, ta samu lamuni ta hannun kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) domin bayadda bashin dala biliyan 3.3.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp