'Yan bindigar da suka sace mutane 31 a Katsina na neman kudin fansa Naira milyan 60


'Yan bindigar da suka sace mutane 31 a kauyen Tashar Nagulle cikin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina sun ce ba za su sako wadannan mutanen ba sai an ba su kudin fansa Naira milyan 60.

Al'ummar yankin ne dai suka sanar da hakan ga jaridar Premium Times a Katsina.

A daren Lahadin da ta gabata ne dai wasu mahara dauke da makamai sun afka kauyen Tashar Nagulle sanye da kayan sojoji, inda suka yaudari al'ummar kauyen cewa su jami'an tsaro ne an turo su ne su kare rayukansu. Sai da mutanen kauyen suka nutsu, sai suka tattara su suka nufi daji su.

'Yan ta'addar dai sun yi amfani da wayar daya daga cikin mutanen da aka sace, suka kira iyalansa, suka nemi da su kai wa Mai Unguwar kauyen don su yi magana da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post