Wani dan sanda da ke aiki karkashin rundunar yan sanda ta jihar Kaduna ya ki karbar cin hancin Naira miliyan 1 da wani kwararren mai garkuwa da mutane ya bashi.
Bayanai sun ce yan sanda sun yiwa dan
garkuwa da mutanen kofar rago ne a wani Otal mai suna Tafa, kuma nan take yayi wa
dan sandan tayin naira miliyan 1 cikin kudin fansar da ya karba, sai dai dan
sandan ya ki karba.
Ko da yake jawabi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ASP Mansir
Hassan ya ce sun sami bayanan sirri ranar 19 ga watan da muke ciki na Agusta
cewa dan garkuwa da mutanen ya sauka a wannan Otal din nan take kuma suka aike
da jami’an su inda suka kama shi.
ASP Mansir ya ce an yi nasarar kwato sama
da naira miliyan 2 da dubu 350 a hannun mai garkuwa da mutanen da aka bayyana
sunan sa da Bello Muhammad mai shekaru 28 dan asalin jihar Zamfara.
Rahoton binciken farko-farko na yan sanda
ya nuna yadda dan bindigar ya shaida musu cewa yana cikin ‘yan ta’adda da ke
addabar yankin dajin Kagarko na jihar Kaduna.