Yadda gwamnatin Kebbi ta tube rawanin Hakimai

 





Gwamnan jihar Kebbi Dr. Naisr Idris


Gwamnatin Kebbi ta sallami wasu dagatai guda uku da ke karkashin masarautar Gwandu daga kan mukaman su, a sakamakon kama su da laifin cin amanar gwamnati, barin guraren aikinsu ba tare da izini ba, wasa da aiki da kuma cin hanci da karbar rashawa.

Da yake sanar da sallamar dagatan guda uku shugaban hukumar kula da kananan hukumomi ta jihar Alhaji Masur Shehu ya ce kokar ta su na karkashin dokokin kula da da’ar ma’aikata ta jihar.

Dagatan da aka kora sun hadar da Alhaji Lawal Yakubu, Mai Arewan Yeldu da Malam Ahmed Sani Sarkin Gabas din Geza da kuma Alhaji Tukur Aliyu Jagwadejin Bakuwe.

Shehu ya ce hukumar ta jima tana bibiyar ayyukan dagatan kuma ta tattara gamsassun hujojjin da suka tabbatar da cewa kora ce kadai hukuncin su.

Ya kuma ce kafin daukar wannan mataki sai da gwamnati ta tuntubi majalisar masu rike da sarautar gargajiya, kuma suka bada wannan shawara.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp