Shugaba Vladimir Poutine na Rasha ya karbi bakuncin takwaransa na rikon kwaryar Chadi Mahamat Idriss Deby a fadar sa da ke Moscou
Batutuwa da dama ne dai aka tattauna a tsakanin shuwagabannin a yayin wannan ziyara
Kasar Rashar dai na dada samun karbiwa a wajen wasu kasashen Afirka masamman rainon Faransa wadanda dangantaka ke kara tsami tsakanin su da uwar gijiyar tasu
Kazalika wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babbar kishiyar Rasha a Duniya wato Amurka ke son cigaban da rike matsayin ta a wajen kasashen na Afirka domin kuwa ko a cikin wannan mako sai da sakataren harakokin wajen ta Antony Blinken ya ziyarci kasashe hudu na nahiyar ciki kuwa har da Najeriya