Ƙungiyar matan ‘yan sanda sun raba awaki ga zawarawa a Kano


Kungiyar matan jami’an ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano, ta raba awaki 137 ga matan da mazajensu suka mutu da kuma marasa galihu a jiya Lahadi, domin bunkasa rayuwarsu

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano.

Shugabar ƙungiyar Aisha Gumel wacce kuma ita ce uwargidan kwamishinan 'yan sandan jihar, ta ce matakin wani aiki ne na yau da kullun na tallafawa iyalan ma'aikatan da suka mutu da waɗanda sukai ritaya da sauran marasa galihu a cikin al'umma.

Aisha ta gabatar da takardar shaidar koyon sana’o’i ga ‘yan kungiyar sama da 100 da suka samu horo tare da daukar nauyin fara sana’o’i daban-daban daga kungiyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp