Gwamnan jihar Fulato Celeb Mutfwang ya ayyana kwanaki 7 a matsayin ranakun da za’a gudanar da alhinin mutanen da suka mutu sama da 150 a sakamakon wani mummunan hari da wasu mutane suka kai musu.
Yayin jawabinsa na Sabuwar
shekara, gwamnan yace za’a fara wannan alhini ne daga ranar 1-7 ga watan Janairun
da muke ciki.
Bayan wannan sanarwa gwamnan ya kuma yiwa wasu daurarrun gidan
yari uku afuwa ta hanyar rage musu yawan shekaru da aka yanke musu, ciki har da
wani Musa Danladi da aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Ya ce ba shakka jihar ta karkare shekarar 2023 cikin tsananin
bakinciki da alhini, don haka wadannan mutane sun chanchanci a ware ranakun don
karrama su.
A tsakanin watan
Aprilu zuwa Yuni masu dauke da makamai sun kashe mutane sama da 400 a jihar
kadai, sai dai na baya-bayan nan shine mafi muni.
Bayanai sun nuna cewa ranar 24 ga watan Disamban da ya gabata ‘yan
bindiga sun kai hari kauyukan Ndun, Ngyong, Murfet, Makundary, Tamiso, Chiang,
Tahore, Gawarba, Dares, Meyenga, Darwat, and Butura Kampani duk a kananan
hukumomin, Barkin Ladi da Bokkos.