Gwamnatinmu ta dauki hanyar kawo karshen matsalar tsaro- Bola Tinubu


 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sanar da cewa gwamnatin sa ta taka rawar gani wajen takaita matsalolin tsaro duk kuwa da hare-haren da ake ci gaba da kaiwa sassan kasar.

Shugaba Tinubu na wadannan kalamai ne kasa da makkonni biyu bayan da yan bindiga suka kai wani mummunan hari jihar Plateau da ke tsakiyar kasar.

Yayin jawabin sa na sabuwar shekara, Shugaban kasa yace tun bayan da ya karbi office gwamnatin ta yi iya bakin kokarin ta wajen ganin irin saukin da aka samu a sassan kasar da hare-hare suka yi kamari.

Tinubu ya ce hare-hare da ake samu nan da can shine dalilin da ya sa gwamnatin ba zata yi ikirarin kakkabe ta’addanci kai tsaye ba, amma tabbas an sami ci gaba.

Inganta fannin tsaro na cikin manyan manufofin shugaban kasar takwas da ya sha alwashin ganin ya sharewa ‘yan Najeriya hawayen su a kai.

Manufofin shugaban 8 sun hadar da tabbatar da tsaron kan iyakoki, tsaron cikin gida, samar da ayyukan yi, habbaka tattalin arziki, gina dan adam, alkinta muhalli yaki da talauci da tsare hakkin al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post