An jarabtu da tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya a shekarar 2023, inji Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce shekarar 2023 ita ce shekarar da ta jawo wahala da tashin hankali a fadin kasashe.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya bayyana hakan a wani sako na bidiyo da aka fitar a jajibirin shekarar 2024.

A cewarsa “bil'adama na cikin zafi. Duniyarmu tana cikin babban matsala. 2023 ita ce shekarar da ta fi zafi a tarihi. mutane na mutuwa ta hanyar karuwar talauci da yunwa. Yaƙe-yaƙe da tashin hankali suna ƙaruwa da yawa Kuma amana ta yi karanci.

“Amma nuna wa juna yatsa da zuwa yaƙe-yaƙe ba za su kawo mafita ba”.

Gutteres ya yi kira da a hada kai cikin gaggawa da kuma hada karfi domin shawo kan kalubalen da ke gabansu. “Dole ne 2024 ta zama shekarar gina amana da maido da zaman lafiya.

“Dole ne mu hada gwiwa domin kawo mafitar wannan rigimar.

“Tare, zamu tashi tsaye wajen yakar wariya da kiyayya da ke haifar da guba game da dangantakar dake tsakanin kasashe da al'ummomi.

“Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da hada kan duniya don samar da zaman lafiya, ci gaba mai dorewa da kare hakkin dan Adam.

“Mu tabbatar da cewa shekarar 2024 ta zama shekarar gina amana kuma muna fatan zaman lafiya.

A halin yanzu, Guterres ya bayyana damuwarsa kan karuwar talauci da yunwa. Yana mai bayyana wadannan kalubalen da ke ci gaba da zama barazana ga rayuwar jama'a a duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post