Majalisar Dinkin Duniya ta nuna bacin ran ta game da harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan jihar Filato a karshen shekarar nan.
Shugaban kula da hakkin bil adama a majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, ya sanar da haka ne a wani jawabi da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.
Mista Volker Turk ya nuna akwai matukar bukatar ayi gaggawar kawo karshen wannan kashe-kashen.
A cewarsa “Ina mai matukar damuwa da jeringiyar hare-haren ‘yan bindiga a kauyuka da-dama da ke jihar Filato."
"Ina kira ga hukumomin Najeriya su binciki wannan lamari da wuri kuma da kyau, bisa doron dokokin kare hakkin Bil Adama, kuma ayi adalci wajen hukunta wadanda aka samu da laifi a kotu."
"Dole a gaggauta kawo karshen wannan zalunci da yake yawon aukuwa. Sannan gwamnati ta dauki matakan kwarai wajen shawo kan asalin matsalolin tare da tabbatar da rikicin ba zai sake faruwa ba." In ji Mista Turk.
A halin yanzu, MDD ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta hana sake faruwar irin wannan ta’adi.