Shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun maka Abba Gida-gida a kotu

Shuwagabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun maka gwamnatin jihar kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan matakin da ta dauka na gina sabbin gadojin sama guda biyu a Tal’udu da Danagundi duk a cikin birni.

Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da kashi 70 cikin 100 na kudaden kananan hukumomi domin gina wadannan sabbin gadoji.

Sai dai Gwamnan a yayin da yake aza harsashin ginin gadar sama da maraicen Juma'a ya yi magana kan hanyoyin samar da kudaden ayyukan inda ya ce al'ada ce da ta faro tun daga magabata na samar da irin wadannan manyan ayyuka ta hanyar yin amfani da asusun hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke gudanarwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post