Bankin Duniya ya sake hasashen samun karuwar ayyukan ta'addanci da matsin tattalin arziki a Katsina da Kaduna

Bankin Duniya ya sake hasashen cewa za a cigaba da samun karuwar ayyukan ta'addanci da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a wasu kananan jihohi 6 na Nijeriya.

Jihohin kamar yadda hasashen bankin duniyar ya nuna su ne na Katsina, Borno, Sokoto, Yobe, Kaduna da Zamfara kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Hasashen na bankin duniya ya ta'allaka ne kan yadda mafiyawan alummomin wadannan yankuna ke gaza zuwa gonakinsu don gudanar da harkokin noma.

Rahoton bankin ya ce kasashen Nijeriya, Chad, Nijar da Mali ne wadannan matsaloli za su iya shafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp