Tsare wani lauya ba bisa ka'ida ba ya ci kujerar wani DPO a Lagos


Rahotanni daga jihar Legas na cewa an dakatar da baturen ‘yan sandan (DPO), na rukunin gidaje na Gowon bisa zarginsa da tsare wani lauya da ke neman adalci ga wanda yake karewa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da dakatar DPOn a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewar Hundeyin, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Adegoke Fayoade, ya ba da umarnin dakatar da jami’in da gaggawa daga sashin.

Post a Comment

Previous Post Next Post