Atiku ya yaba da matakin Tinubu kan su Betta Edu da Sadiya


Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba wa shugaba Tinubu kan dakatar da ministar jin kai Betta Edu da ya yi.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar.

Atiku ya bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa ministar abin a yaba ne ga shugaban kasar.

An dai dakatar da ministar jin ƙan bisa zargir ta da tura Naira miliyan 585 zuwa wani asusu na daban.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp