Tinubu ya rage yawan kudaden da ake kashewa a tafiye-tafiye

 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar da rage yawan kudaden da ake kashewa a tafiye-tafiyensa da na mataimakinsa da karin wasu mukarraban gwamnati.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, inda ya ce wannan sabon tsarin zai shafi tafiye-tafiyen shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da ma uwargidan shugaban kasar da sauran manyan jami’an gwamnati.

Yace tafiye-tafiye zuwa kasashen waje shugaban kasar zai tafi da mutane 20 da aka rage daga mutane 50 a baya, yayin da mataimakin shugaban kasa zai kasance da mutum biyar kawai, sannan kuma uwargidan shugaban kasar da mutane biyar.

Tafiye-tafiyen cikin gida kuwa, shugaban kasar zai samu rakiyar mutane 25, sai mataimakin shugaban kasar zai tafi da mutum 15 yayin da uwargidan shugaban kasa za ta tafi da mutane 10.

Sanarwar ta ce shugaban kasar ya rage yawan kudaden tafiye-tafiyen ne da kaso 60%.

Post a Comment

Previous Post Next Post