Sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya dawo gida Nijeriya bayan ya shafe wasu kwanaki yana jinya a kasar Saudiyya.
Idan za a tuna ranar 7 ga watan Disamba ta shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta amince da nadin Abdullahi Musa, shugaban ma’aikata na jihar ta nada shi rikon kwarya.
Dawowar Sakataren gwamnatin na zuwa ne a daidai lokacin da kotun koli ke shirin yanke hukuncin zaben gwamnan jihar.
Bichi ya sauka a filin jirgin sama na Aminu Kano, ya kuma samu tarba daga 'yan uwa da abokan arziki.
Category
Labarai