Dan majalisar tarayya ya fara gwangwaje al'ummar mazabarsa da ayyukan ci gaba a Katsina


Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina Hon Sani Aliyu DanLami ya ce zuwa karshen watan nan na Janairu, za a fara gudanar da ayyukan hanyoyin da ya sanar cewa za a gudanar a unguwanni daban-daban na karamar hukumar.

Sani Aliyu DanLami na magana da manema labarai dangane da ayyukan samar da ruwan sha da fitilu masu amfani da hasken rana da yake gudanarwa a karamar hukumar.

Ya ce za a gina hanyar da ta tashi daga Kofar Sauri zuwa Lambun Dan Lawal zuwa Yandadi ta wuce zuwa Bye Pass

Haka kuma, ya ce akwai hanyar da ta tashi daga Tashar Rabe zuwa Bye Pass, da wasu hanyoyin da ya ce ya nemo duk za a gudanar da ayyukan su.

Sanı Dan Lami ya ce cikin watanni hudu za a yi aikin a kammala, don haka al’umma su ba da gudunmuwa wajen ganin an yi aiki mai inganci domin ci gaban karamar hukumar da jihar Katsina bakidaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post