Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar Barr Muhyi a ranar Juma'a

Kotun kula da ma'aikata ta CCB da ke zamanta a Abuja, ta sanar da ranar Juma'a 12 ga watan Janairu, 2024 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar Barr Muhyi Magaji Rimin Gado.

Muhyi Rimin Gado dai shi ne shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano PCACC.

Kotun dai ta ba da wannan matsayar ne a Larabar nan bayan zaman da ta gudanar karkashin jagorancin Mai Shari'a Danladi Umar.

Kamfanin Dillancin labaran Nijeriya NAN ya ba da labarin cewa a ranar 16 ga watan Nuwambar 2023, kotun ta tsare Muhyi Magaji Rimin Gado, inda take tuhumarsa da laifuka 10.

Sai dai Barr Muhyi ya kiya amsa laifin, har ma ya nemi a ba da shi beli, karshe kotun ta ba da shi beli kan kudi Naira milyan 5 da masu tsaya masa guda biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post