Gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan Nijar ta sanar da hallaka fararen hula a 'yan kasar bisa kuskure a lokacin da dakarun kasar ke kokarin maida martani ta sama da jiragen yaki daga wani harin ta'addanci da wasu mahara suka kai musu a yankin karamar hukumar Gothèye da ke cikin jihar Tillaberi
Ministan tsaron kasar ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar wacce a cikin ta ya ce lamarin ya faru ne a dare Juma'a wayewar Asabar din nan ta 6 ga watan Janairu