Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya Dakatar da Minister Jinkai, Betta Edu nan take.

 Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu nan take.



Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar cikin wata sanarwa da aka fitar a yau.


Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.




Wasu yan Najeriya sun yi ta kiraye-kiraye ga gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta nata domin a gudanar da cikakken bincike game da zarge-zargen da ake mata.


Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa wani asusun banki da babban akanta janar na ƙasa yaki amincewa da shi.


Shugaba Tinubu a sanarwar da ta fito daga fadar sa ya umurci shugaban hukumar EFCC ya gudanar da bincike sosai kan zargin da ake wa Beta Edun.

Post a Comment

Previous Post Next Post