Kafa cibiyoyin koyon sana'o'in hannu zai taimaka a rage yawaitar zuwa ci rani a tsakanin matasa - Mamman Abubakar Danmusa

Tsohon shugaban Majalisar Dokokin tsohuwar jihar Kaduna Alhaji Mamman Abubakar Danmusa ya bayar da shawarar kafa cibiyoyin koyar da sana'oi domin kawo karshen yawan kaura da matasa sukeyi zuwa wasu garuruwa.


Alhaji Mamman Abubakar Danmusa na magana ne a lokacin bikin kaddamarwa da hannanta cibiyar koyar da sana'oi mai azuzuwa biyar da ofisoshin malamai 2 da ya gina a garin Danmusa ga gwamnatin jahar katsina 


Tsohon shugaban majalisar Dokokin ya bayyana cewa ya hananta cibiyar ne ga gwamnatin jiha don samar da kayan aiki da ake bukata ga cibiyar wanda zasu taimaka ma matasa marassa aikin yi koyon Sana'oi hannu.


Alhaji Mamman Abubakar Danmusa wanda ya samu wakilcin babban Dan'sa Nuradden Mamman Danmusa yace ya yanke shawarar kafa cibiyar horar da sana'oi ne don tallafawa matasa su zamo masu amfani acikin al'umma.


Daga nan sai ya bukaci masu hannu da shuni dasu rika kafa irin wadannan cibiyoyin don karfafama matasa gwaiwa wadanda sune kashin bayan al'umma.


Alhaji Mamman Abubakar Danmusa wanda ya taba zama mataimakin shugaban majalisar dattawa a jamhuriyya ta biyu ya bukaci matasa da su amfani da cibiyar domin dogaro da kai.


A jawabinshi bayan karbar makullin cibiyar amadadin shugabar hukumar bunkasa Sana'oi Aisha Aminu malumfashi, Daraktan shiyya na hukumar Alhaji kabir Abdullahi kofar soro ya yabama hangen nesan Mamman Danmusa bisa kafar cibiyar da yayi hadi da rawar da yake takawa don ciyar da yan'kin dama jiha baki bdaya.


Ya kuma bayyana kafa cibiyar amatsayin sadakatu jariya ga Mamman Abubakar Danmusa, inda ya jaddada cewa cibiyar zata samarwa matasa a bubuwa a yan'kin.


A jawabin godiya magajin malam Hakimin Danmusa Alhaji Darda'u muaazu Abubakar Danmusa wanda ya samu wakilcin wakili Gurza Alh Darda'u Gambo Danmusa ya yabama da irin gudumuwar da yake bayar wa ga cigaban yankin.


A jawabansu daban daban Sarkin kasuwa Bishir yusufa da murtala Amadu mai shanu da kuma Nura Abdu sun yaba da gudumuwar da mamman Abubakar Danmusa yake tallafama Al'ummar yankin, tare da rokon Allah ya sakama shi da mafificin allhairi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp