NDLEA ta kama matar da ke kai wa 'yan ta'adda makamai a Katsina


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta sanar da kama wata mata mai suna Bilkisu Sulaiman da ake zargi da safarar makamai ga 'yan ta'adda a jihar Katsina.

Kamar yadda sanarwar da ta fito daga kakakin hukumar na kasa Femi Baba Femi, ta ce an kama matar mai shekaru 28 na safarar makaman ne kan titin Zaria-Kano, inda take burin kai makaman a kauyen Kakumi na karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Hukumar ta ce an samu matar da harsasai 249 da aka kulle a cikin bakar leda aka saka cikin karamar jikkar hannu.

Femi ya ce bayan kama matar, an kai ta Ofishin 'yan sanda na jihar Kaduna don karasa bincike a kanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post