Shin wane ne Engr. Abba Kabir Yusuf, gwamnan Kano?


Shekaru 61 da suka gabata aka haifi gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf a ranar 5 ga Janairun 1963 a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano.

Engr Abba Kabir Yusuf ya halarci makarantar firamaren garin Sumaila da makarantar sakandaren Dawakin Tofa da kuma sakandaren Lautai dake Gumel din jihar Jigawa a halin yanzu kuma a can ne ya kammala karatun sakandare a shekarar 1980. 

Gwamna Abba ya samu satifiket na diploma a Kwalejin Tarayya da ke Mubi jihar Adamawa a halin yanzu, sai ya yi babbar diploma wato HND a Kaduna Polytechnic. 

Kwararren Injiniyan ya kuma kara fadada karatunsa a jami'ar Bayero da ke Kano a inda ya samu shaidar PGD. 

Ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da kuri’u 1, 019, 602 Sai dai wannan nasara ta fara girgidi a hannunsa tun lokacin da kotun sauraren kararraki ta tsame kuri’u 165,000 da ce babu hatimin hukumar zabe a jikin su, lamarin da ya sanya kotun ayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara wanda da farko INEC ta ce ya samu kuri’u 890,705. 

Karin bayani: Ranar sanin makomar 'Gawuna Is Coming ko Kwankwasiyya Daram' a Kano

Duk da yawan mutanen da suka zabe shi, masu adawa da Engr. Abba Kabir Yusuf na zargin mutum ne wanda ba ya iya daukar hukunci na kashin kansa, wato dai kawia dan amshin shata ne ga mai gidan sa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso. 

A yayin da masu goyon bayansa ke cewa hakan ba komai bane sai kwarewa a biyayya, kasancewar sa mutum mai cike da biyayya da kawaici tare da mutunta mutum ba tare da gadara da ake zargin wasu shugabanni da aikatawa ba. 

A shekarar 1999 bayan an dawo dimokradiyya, Gwamnan jihar Kano a wancan lokacin Rabi'u Musa Kwankwaso ya nada Abba Gida-Gida mukamin hadimi na musamman wato PA ga Gwamna, Mukamin da Abba ya ci gaba da rikewa har bayan Kwankwason ya zama ministan tsaron Nijeriya a wa'adi na biyu na mulkin Obasanjo daga 2003-2007. 



Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran darikar Kwankwasiyya ya nada Abba mulkin kwamishinan ayyuka na jihar Kano, a shekarar 2011 lokacin da ya dawo kan karaga a karo na biyu a matsayin Gwamna. 

A shekarar 2018, jam'iyyar PDP ta tsayar da Abba a matsayin dan takarar Gwamnan Kano, Wanda suka Kara da Gwamna a wancan lokacin Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC bayan an raba gari tsakanin Kwankwaso da Ganduje.  Sai dai zaben a karshe ya kare da Inconclusive, kuma bayan kamala shi ne hukumar zabe ta ayyana Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben 2019. 

Sai a shekarar 2022, Abba Kabir Yusuf ya bar PDP ya koma NNPP. Wannan ke-tare da watakila kuskuren da ya yi kamar yadda kotun daukaka kara ta bayyana na rashin karbar katin jam’iyyar NNPP a lokacin da ya sauya sheka na cikin dalilan da suka sanya ita kotun soke nasarar da Abba ya samu a matsayin gwamna. 




Tun da farko dai ya yi fafatawa mai zafi da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC a zaben na 2023. 

A yanzu Abba Gida-Gida da magoya bayansa sun zura ido su ji hukuncin da kotun koli za ta yanke kan rusa nasararsa har sau biyu da lauyoyin jam’iyyar APC suka yi nasarar samu a kotuna biyu.

Abba, shi ne gwamna na 8 da aka zaba a jihar Kano tun daga shekara ta 1960 zuwa yanzu, Kafin shi zuwan Abba, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ne aka fara zaba a shekarar 1979 a jam'iyyar PRP, sai Alhaji Abdu Dawakin Tofa sai kuma Alhaji Sabo Bakin Zuwo, dukkaninsu 'yan jam'iyyar PRP. Sanata  Kabiru Ibrahim Gaya ya take musu baya a jam'iyyar  NRC. Daga nan sai Rabi'u Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da kuma Abdullahi Umar Ganduje.

Daga cikin jiga-jigan da suka taya Gwamna Abba murnar zagayowar ranar haihuwarsa harda shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya yi wa Abba fatan samun koshin lafiya da tsawon rai a duniyar nan. Sai kuma mai gidansa, wato, Dr Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya ce biyayya ta yi wa Abba Kabir rana musamman ganin yadda ya samu daukaka tun daga karamin dan siyasa har yanzu ga shi a matsayin gwamnan jihar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp