Hukumar kula da ayyukan ‘yan
sanda ta kasa ta ce mutane dubu 30 kachal zata dauka aiki, cikin sama da dubu
400 da suka nemi aikin a bana.
Ta cikin wata sanarwa da
shugaban hukumar Solomon Arase ya fitar ta ce sama da mutane dubu 400 ne suka
nemi aikin dan sanda cikin makonni 6 kachal da bayar da sanarwar.
Hukumar ta ce zata fara tantance
wadanda suka nemi aikin don tsamo wadanda suka chanchanta a gobe litinin 8 ga
watan da muke ciki na Janairu.
Arase wanda tsohon Supeton ‘yan
sanda ne ya ce ma’aikatan hukumar zasu zabi ma’aikata ne bisa chanchanta, don
haka ya gargadi masu yunkurin amfani da sanayya wajen samun aikin da su kuka da
kansu matukar aka kama su.
Category
Labarai